Kotu Ta Ba da Sammacin Kama Tsohon Minista Kabiru Turaki SAN

Wata Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja   ta bayar da sammacin kama (bench warrant) a kan Kabiru Tanimu Turaki (SAN), tsohon Ministan a  Najeriya.

 

 

 

 

Kotun da Mai Shari’a Keke Meke ke jagoranta ta kuma ƙi amincewa da buƙatar lauyan kariya wadda ta nemi a soke tuhumar da ake yi wa Turaki.

 

 

 

 

 

Ana zargin Turaki ne da ba wa ‘yan sanda bayanan ƙarya, kuma ana sa ran Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda za ta gurfanar da shi a gaban kotu domin amsa tuhume-tuhumen.

 

 

 

 

 

 

Tun da farko, an fara shari’ar ne a wata kotu da ke Zuba, amma Turaki bai bayyana a kotu ba domin karɓar tuhumar da ake yi masa. Daga bisani, lauyoyinsa sun rubuta ƙorafi a kan alkalin, tare da neman a mayar da shari’ar wani kotu.

 

 

 

 

 

 

A hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, Mai Shari’a Meke ya ce babu wata hujja da ta cancanci rashin zuwan Turaki kotu, yana mai cewa Turaki ya san da zaman shari’ar, don haka kotu ta bayar da umarnin a kama shi.

 

 

 

 

 

A yayin zaman, lauyan masu gabatar da ƙara, Rabiu Umar, ya yi adawa da roƙon lauyan kariya, Abdulaziz Ibrahim, wanda ya nemi kotu ta soke tuhumar.

 

 

 

 

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga Afrilu domin ci gaba da shari’ar.

You might also like
Leave a comment