Kungiyar Lauyoyin Gwamnati ta kasa Reshen jahar Kano Ta Fara Yajin Aikin sai baba ta gani

Kungiyar Lauyoyin Gwamnati ta Najeriya reshen Jihar Kano (Law Officers Association of Nigeria  ta sanar da fara yajin aiki sai baba tagani  daga yau  Talata, 11 ga Maris, 2026, sakamakon korafe-korafe da suka ce gwamnatin jihar ta kasa magance su.

 

 

 

 

Shugaban kungiyar a Kano, Barrista Aminu Abdullahi Shamsi, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano.

 

 

Ya ce daukar wannan mataki ya zama dole bayan shekaru na sakaci da kuma alkawuran da gwamnati ta yi amma ba a cika ba.

 

 

 

A cewarsa, kungiyar ta rubuta wasiƙa zuwa ga Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano mai taken “Sanarwar Fara Yajin Aikin sai baba tagani, inda ta tuna da kokarin tattaunawa da shiga tsakani da aka yi a baya amma ba tare da samun sakamako mai kyau ba.

 

 

 

Kungiyar ta ambaci wasu wasiƙu da ta aika tun farko, ciki har da wasiƙa mai lamba LOAN/KN/16/25 da aka rubuta ranar 18 ga Yuni, 2025, tare da rahoton wani kwamitin fasaha na mutane takwas da gwamnatin jihar ta kafa domin duba matsalolin.

 

 

 

 

Sai dai kungiyar ta ce duk da cewa gwamna ya amince da wasu shawarwarin kwamitin, ba a taba aiwatar da rahoton ba.

 

 

Haka kuma sun ce wani taron sasanci da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da kuma Babban Lauyan Jihar suka kira bayan sanarwa ta biyu da kungiyar ta bayar ranar 29 ga Janairu, 2026, bai haifar da wani sakamako ba.

 

 

 

Kungiyar ta kara da cewa duk da sun dakatar da wani yajin aiki da suka shirya yi a watan Fabrairu 2026 bayan roƙon gwamnati tare da ba ta wa’adin kwanaki 28, har yanzu babu wani abu da aka aiwatar daga cikin alkawuran da aka yi.

 

 

 

 

 

Barrista Shams ya ce bayan wani babban taron kungiyar da aka gudanar 9 ga Maris, 2026, mambobin kungiyar suka yanke shawarar fara yajin aiki bisa tanadin sashe na 41 da 42 na Dokar Rikicin Ma’aikata ta 1976.
Manyan Matsalolin da Suke Kuka da Su
Kungiyar ta lissafa wasu daga cikin matsalolin da suka sa suka shiga yajin aiki, ciki har da:
Rashin biyan albashi da alawus cikin adalci kamar yadda ake yi wa takwarorinsu a Jihar Jigawa

 

 

 

 

Rashin biyan wasu alawus-alawus tun daga 2017
Rashin biyan domestic servant allowance
Cire sit-in allowance da responsibility allowance ga wasu daraktoci
Rashin biyan watanni biyu na bashin albashi ga sabbin State Counsel
Rage kudin fansho ga wadanda suka yi ritaya bayan aiwatar da mafi karancin albashi na N71,000

 

Rashin wadatattun ofisoshi da bandaki ga ma’aikata
Rashin samar da motocin aiki ga State Counsel
Rashin biyan N170,000 na kudin mai da alkalan majistare da na kotunan shari’a ke samu tun daga Janairu 2024

 

 

Rashin aiwatar da kara darajar mukami ta atomatik (automatic promotion) tun 2022
Tilasta musu shiga tsarin inshorar lafiya na KACHMA duk da cewa ya kamata ya kasance na son rai

 

 

 

Kungiyar ta kuma bukaci a sanya matakin shiga aiki ga sabbin lauyoyi a matakin GL10, tare da hada albashinsu da alawus dinsu kamar yadda ake yi wa alkalan majistare.

 

 

 

Barrista Shams ya jaddada cewa yajin aikin ba gaggawa aka dauke shi ba, sai bayan shekaru na hakuri da kokarin tattaunawa da gwamnati.

 

 

Ya kuma gargadi cewa dukkan lauyoyin gwamnati a jihar za su dakatar da duk wani aiki har sai an biya bukatunsu.

 

 

 

 

Ana sa ran wannan yajin aiki zai takura harkokin shari’a a Jihar Kano, domin lauyoyin gwamnati ne ke wakiltar gwamnati a kotuna da kuma tafiyar da wasu muhimman harkokin shari’a.

You might also like
Leave a comment