Jami,an hukumar NDLEA ta tarwatsa wasu wuraren sayar da miyagun ƙwayoyi a Kano, ta kuma kama mutane 56

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Kano ta ce ta tarwatsa wurare da dama da ake sayar da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar, tare da kama mutane 56 a wani samame da aka gudanar cikin kwanaki uku.

 

 

 

 

 

Mai magana da yawun rundunar a Kano, ASN Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano.

 

 

 

 

Ya ce kwamandan NDLEA na jihar, Mista Dahiru Yahaya-Lawal, ya bayyana cewa an kama mutanen ne yayin wani samame da aka kai, a matsayin wani ɓangare na “Operation Ramadan Mubarak”, domin tabbatar da zaman lafiya da kuma rage yawaitar miyagun ƙwayoyi a Kano a lokacin Ramadan da ma bayan watan.

 

 

 

 

Ya ce tsakanin 6 zuwa 8 ga Fabrairu, jami’an NDLEA sun kai samame wuraren da aka dade ana zargin ana sayar da miyagun ƙwayoyi a yankunan Kofar Mata, Fagge, Kasuwar Rimi, Medile, Badawa da Sabon Gari a jihar.

 

 

 

 

A cewarsa, samamen ya kuma bazu zuwa wasu wurare a cikin birnin Kano da ma wajen birnin domin rusa cibiyoyin rarraba miyagun ƙwayoyi ba bisa ka’ida ba.

 

 

 

Ya ce:
“Wannan samame ya kasance ci gaba da ƙoƙarin da muka dade muna yi na matsa lamba ga ƙungiyoyin masu aikata laifukan miyagun ƙwayoyi da suka jima suna aiki a waɗannan al’ummomi.

 

 

 

 

“An tsara wannan aiki ne domin katse hanyoyin rarraba miyagun ƙwayoyi tare da dawo da zaman lafiya a unguwannin da ke fama da matsalar.”

 

 

 

 

Yahaya-Lawal ya ƙara da cewa a yayin samamen jami’an sun kwato miyagun ƙwayoyi iri-iri da suka haɗa da wiwi (cannabis sativa), Exol-5, diazepam da pregabalin, da sauran kwayoyi da aka haramta.

 

 

 

 

Ya ce wannan kamen ya zama babban koma baya ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a yankin, kuma yana nuna ƙudirin hukumar na kawar da miyagun ƙwayoyi a cikin al’umma.

 

 

Haka kuma, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Yunusa Yasin mai shekaru 30 daga yankin Badawa, yana da alaƙa da wani kisan kai da ya faru shekaru biyar da suka wuce.

 

 

 

Ya ce an miƙa shi ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

 

 

 

 

Kwamandan ya sake jaddada kudirin NDLEA na ganin Kano ta zama jiha mara miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumar bayanai kan masu safarar miyagun ƙwayoyi domin taimakawa wajen kare al’umma

You might also like
Leave a comment