Yakin Iran da Isra,ila Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe ‘yan ƙasarta daga Iran
Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe ‘yan ƙasarta daga ƙasar Iran da suka nuna buƙatar a dawo dasu gida, tare da raka su ta kan iyakar ƙasar Armeniya domin tabbatar da tsaron lafiyarsu a yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ce ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a jiya Talata.
Shugabar ta kuma tabbatar da cewa kawo yanzu babu wani ɗan Najeriya a Iran da rikicin da ke faruwa ya shafa, inda ta ce jami’an ofishin jakadancin suna can a bakin iyakar ta Iran da Armenia domin karɓar da kuma taimakawa waɗanda ke son a kwaso su daga Iran su tsallaka iyakar.
Dangane da soma tasowar jiragen da za a dawo da su gida kuwa, Shugabar ta ce a halin yanzu sararin samaniyar yankin ba shi da tsaro, amma ta tabbatar wa ‘yan Najeriya mazauna yankin Gabas ta Tsakiya cewa, tawagar gwamnatin tarayya na shirye-shiryen kwaso su.
Ta ce, “an fara samun jirgin da ya taso daga ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa Legas kwanaki biyu da suka gabata kafin wani sabon hari da ya sa aka rufe sararin samaniyar kasar.”
Ta ƙara da cewa “da zarar an bude sararin samaniyar, tawagar gwamnatin tarayya da ta ƙunshi jami’ai daga ma’aikatu daban-daban za su shiga aikin kwaso mutanen.”
Wannan matakin da ya biyo bayan ƙaruwar rikicin da ya fara tun daga ranar 28 ga watan Fabrairu bayan wani harin soji da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran.