Ministan tsaron Najeriya yana tantaunawa da manyan hafsoshin tsaro nasar

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya gayyaci duka manyan hafsoshin sojin ƙasar zuwa ofishinsa kan ƙaruwar hare‑haren ƴanbindiga a baya-baya nan kan sansanonin soji a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

 

 

 

 

 

Taron wanda ke gudana a ma’aikatar tsaron ƙasar ya samu halartar babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Olufemi Oluyede, da babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar Waidi Shaibu.

 

 

 

 

 

Sauran sun haɗa da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sunday Aneke da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Idi Abass da wakilan Hukumar leƙen asiri ta Kasa (NIA) da wasu da dama.

 

 

 

 

 

Rahotonni sun nuna cewa aƙalla manyan kwamandoji guda uku sun rasa rayukansu a hannun ƴanbindiga a Borno kwanan nan.

 

 

 

 

 

Baya ga kwamandojin da suka mutu, dubban sojoji sun rasa rayukansu yayin da aka sace ɗaruruwan fararen hula.

 

 

 

 

 

Gabanin fara taron, CG Musa ya ce sun yanke shawarar sake duba dabarun yaƙi da ‘yanbindiga duk da cewa rundunar.

You might also like
Leave a comment