Majalisar Wakilai ta Najeriya ta ba da shawarar tarar Naira miliyan 10 ko daurin shekaru biyu ga masu shiga jam’iyya biyu

Majalisar Wakilai ta Nigeria  ta amince da wani gyara ga dokar zaɓe da zai sanya tsauraran hukunci ga duk wanda aka samu yana da rajista a jam’iyyun siyasa fiye da ɗaya.

 

 

 

 

Gyaran da aka yi wa Electoral Act 2022 ya tanadi hukunci na laifi ga masu memba a jam’iyyun siyasa biyu, inda za a iya cinsu tarar Naira miliyan 10, ko daurin shekara biyu a gidan gyran hali ko kuma duka biyun idan kotu ta same su da laifi.

 

 

 

 

Sabon  tanadin ya bayyana cewa duk wanda aka gano yana da rajista ko yana gudanar da harkokin siyasa a jam’iyya fiye da ɗaya, za a soke dukkan membobinsa a jam’iyyun, sannan kuma ba za a ba shi sahihiyar membobinsu ba har sai ya gyara matsayinsa yadda doka ta tanada.

 

 

 

 

‘Yan majalisar sun ce an kawo wannan gyara ne domin ƙarfafa ladabtarwa a cikin jam’iyyun siyasa da kuma kare sahihancin tsarin zaɓe a Najeriya.

 

 

 

 

Haka kuma, an ce dokar na da nufin rufe gibin da wasu ‘yan siyasa ke amfani da shi wajen ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyun siyasa da dama lokaci guda domin samun tasiri a fannoni daban-daban.

 

 

 

 

 

Masu goyon bayan kudirin sun bayyana cewa wannan gyara zai taimaka wajen ƙarfafa tsarin jam’iyyun siyasa a ƙasar, musamman yayin da ake ganin sauyin sheƙa daga jam’iyya zuwa wata yana ƙaruwa kafin manyan zaɓuɓɓuka masu zuwa.

 

 

 

 

Idan  Senate ta amince da kudirin, sannan shugaban kasa  ya sanya hannu, dokar na iya zama ɗaya daga cikin mafi tsauri da aka taɓa kafa wa masu karya dokar membobinsu a jam’iyyun siyasa a Najeriya.

You might also like
Leave a comment