Kwammanshinan tsaron da harkokin cikin gida,Air vice marshan ibrahim umaru ya aje aikinsa na kwammanshina na gwamnatin jahar kano
Kwamishinan ya ajiye aikin ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf yake gudanar da bikin komawa jam’iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.
Tsohon sojan na sama ya bar gwamnatin ne domin cigaba da nuna goyon bayansa ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwanso.
A wata takarda da ya fitar, ya ce “ganin yadda abubuwa suke faruwa, ina ganin zai fi kyau in ajiye muƙamina in koma gefe.”
Ibrahim Umaru ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagoransa kuma abin koyi, “kuma koyi da shi ne wajen aiki da adalci da fifita buƙatun al’umma.”