Gawuna da Garo ba za su yi takara da Abba ba – Ganduje

 

Toshon shugaban jam’iyyar APC na Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce tsoffin waɗanda suka yi wa APC takarar gwamna da mataimaki a jihar cikin APC ba za su yi takara da Abba Kabir Yusuf ba.

 

 

 

 

Yayin da yake jawabi a wurin taron komawar Abba APC, Ganduje – wanda shi ne ubangidan Gawuna da Garo – ya ce sun tabbatar masa cewa ba za su yi takara da Abba a 2027 ba.

 

 

 

A shekarar 2023 takara ta yi zafi tsakanin Gawuna da Abba, inda har aka sake zaɓe a wasu akwatunan jihar.

 

 

Abba Kabir Yusuf ya koma APC ne bayan raba gari da jam’iyyar NNPP da Sanata Rabi’u Kwankwanso ke jagoranta.

 

You might also like
Leave a comment