Rundunar Sojoji nigeria ta gano masana’antar ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba a jahar Nasarawa

Rundunar sojin Najeriya ta ce Sojojinta na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun “gano wata masana’antar ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba da ke a ɓoye a yankin Agwatashi da ke ƙaramar hukumar Doma a Jihar Nasarawa.”

 

 

 

Sojojin sun gano wurin ne yayin da suke gudanar da aikinsu na sintiri domin hana masu aikata laifuka yin kutse da samun ‘yancin motsi.

 

 

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X.

 

 

Rahotanni sun nuna cewa wurin an ɓoye shi ne domin ƙera makaman da ake bai wa masu aikata laifuka a yankin da ma wajen sa.

 

 

Da isar sojojin wurin, wasu mutane da ake zargi sun tsere suna ganin sojojin amma daga baya aka kama mutum ɗaya ɗan shekara 26 daga ƙauyen Arusu a ƙaramar hukumar Kokona, yayin da yake ƙoƙarin tserewa ta hanyar ɓoye kansa a kan wata bishiya.

 

 

Binciken da aka yi a wurin ya kai ga gano bindigogi guda shida da aka ƙera da kayan aiki da na’urorin da ake amfani da su wajen ƙera makamai da kuɗi da kuma wayar salula da aka samu a hannun wanda aka kama.

 

 

Binciken farko ya nuna cewa “wurin na samar da makamai ga ‘yan ta’adda a ciki da wajen yankin.”

 

 

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara ya buƙaci sojojin su da su ci gaba da dogaro da sahihan bayanan sirri domin tarwatsa cibiyoyin aikata laifuka.

 

 

 

Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro mai ɗorewa da bunƙasar tattalin arziki.

 

You might also like
Leave a comment