Matsalar tsaro tasa Gwamnatin jihar Kogi ta rufe wasu kasuwanni
Gwamnatin jihar Kogi ta sanar da rufe wasu kasuwanni da tashoshin motoci na wucin gadi a sassan jihar, a wani mataki na tsaurara matakan tsaro
Wata sanarwa da hukumomin jihar suka fitar a ranar Lahadi ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta tsaro da fatattakar ƴan bindiga, da sauran masu aikata laifuka.
”Rufewar na wucin gadi, wanda za ta fara aiki nan take, an yi shi ne da nufin katse hanyoyin samun kayan aiki, da takaita zirga-zirgar kayan masarufi, da hana masu aikata laifuka da masu ba su bayanan sirri damar samun kayan abinci da sauran nau’ikan tallafi yayin da ake gudanar da ayyukan tsaro”. In ji sanarwar
Jihar Kogi na da iyaka da jihar Kwara, inda aka yi wa sama da mutane 100 kisan gilla a garin Woro a makon da ya gabata.
Kwanan nan, an kuɓutar da mutane 16 da aka yi garkuwa da su daga sansanin wani fitaccen shugaban ƴan bindiga, Kachalla Battijo, da ke dajin Tunga.
Jami’an tsaro sun mamaye sansanin ƴan bindigar, inda ake ci gaba da gudanar ayyukan tabbatar da tsaro a yankin.