Mataimakin shugaban kasa kashim Shettima zai jagoranci taron majalisar tattalin arzikin Najeriya

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima zai jagoranci taron majalisar tattalin arzikin ƙasar da za a gudanar ranar Litinin a Abuja.

 

 

 

Cikin wata sanarwar da fadarsa ta fitar ta ce maƙasudin taron shi ne ƙarfafa aiki tare don bunƙasa tattalin da haɓaka ci gaba a jihohin ƙasar 36.

 

 

 

An tsara za a gudanar da taron a zauren fadar shugaban ƙasar da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar litinin

 

 

 

Taron zai samu halartar gwamnonin jihohin ƙasar 36 waɗanda su ne ƴanmajalisar da kuma masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arzikin ƙasar.

 

 

 

Taron na kwana biyu – wanda ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya shirya – zai mayar da hankali a fannonin zuba jari da musayar dabaru tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.

You might also like
Leave a comment