Rundunar yan sanda jahar kebbi tace ta dakile wani harin lakurawa
Rundunar yan sandan jihar kebbi da hadin gwiwar sojoji dakuma sauran hukumomin tsaro sun dakile wani hari da ake zargin lakurawa ne suka kai a karamar hukumar bunza, wanda jami’an tsaro sukayi nasarar kashe mutum daya daga cikin yan bindigar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan na jihar kebbi ya fitar yace sunyi musayar wuta da yan bindigar inda daya daga cikin lakurawan ya rasa ransa tare da kwato Babura guda hudu ake zargin sunyi amfani dasu
Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun shiga kauyen tungar babu lada, inda suka harbi wani magidanci mai shekaru 35 wanda yayi sanadin rasa rayuwarsa tare da daukar shanun sa sai dai jam’an tsaro sun sun samu nasarar daukar matakin da ya dace wajen dakile dukkan yunkinrin yan ta’addar.
Rundunar tace zata cigaba da sintiri da aikin liken asiri domin kare rayuwaka da dukiyoyin al’ummar jihar kebbi