Rundunar Sojoji nigeria Sun Ceto Mutane 3 da Aka Sace, Sun kuma Dakile wani Hari a Bama
Sojojin Operation HADIN KAI sun ceto wasu fararen hula uku da aka sace bayan sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.
A cewar wata sanarwa da Laftanar Sani Abubakar Muhammad, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soji, Brigade ta 21 Special Armoured, wannan aiki ya gudana ne a ranar Lahadi, 29 ga Maris, 2026.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’adda da ake zargi sun sace mutanen ne yayin da suke dibin itacen girki a yankin BOCOBS, kafin sojoji su tashi cikin gaggawa bayan samun sahihin bayanan sirri.
An ce an tura wata rundunar kai dauki daga Bataliyar 202, tare da hadin gwiwar sojojin garrison da kuma ’yan sa-kai, inda suka yi artabu da maharan.
Sanarwar ta ce :“Da isarsu, sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan tare da murkushe su, lamarin da ya sa suka gudu cikin rudani saboda karfin wutar da sojoji suka yi amfani da ita.”
Bayan haka, sojojin sun gudanar da bincike a yankin inda suka samu nasarar ceto dukkan mutanen uku ba tare da sun ji rauni ba, tare da kwato mujallar bindigar AK-47 guda daya da kuma harsasai 30 na 7.62mm.
Rundunar sojin ta ce wannan nasara na nuna jajircewarta wajen kare fararen hula da kuma ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas.