NCC Ta Umurci Kamfanonin Sadarwa na nigeria Su Biya Diyya Ga Masu mu,amala dasu Saboda Mummunan rashin Network da akasamu
Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (Nigerian Communications Commission – NCC) ta umurci kamfanonin sadarwa da su rika biyan diyya ga masu amfani da layukan waya idan aka samu rashin ingancin network a wasu yankuna da ya gaza cimma matakan da aka kayyade.
Hukumar ta bayyana cewa bai dace a rika dora wa masu amfani nauyin matsalar katsewar sadarwa gaba ɗaya ba, musamman idan kamfanonin sadarwa sun kasa cika ka’idojin da aka shimfiɗa na ingancin aiki.
Nnenna Ukoha, Shugabar Sashen Hulɗa da Jama’a na NCC, ita ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a ranar lahadi.
A cewar Ukoha, kamfanonin da aka samu da laifi za su biya diyya kai tsaye ga masu amfani da suka samu matsala, musamman idan sun karya ka’idojin Quality of Service (QoS) da kuma Key Performance Indicators (KPIs).
Ta kuma ce za a tilasta wa MNOs su biya diyya idan aka samu mummunan network a cikin wani lokaci da aka kayyade a wasu yankuna.
Za a bayar da diyya ne ta hayar icredit na airtime, wanda za a lissafta bisa la’akari da irin yawan kudin da mutum ke kashewa a layinsa, da kuma kasancewarsa a cikin Karamar Hukumar da aka samu matsalar sadarwa.
Hukumar NCC ta ce wannan umarni yana cikin manufarta ta sanya mai amfani (consumer) a tsakiyar tsarin sadarwa na Najeriya. Ta ce sadarwa a yau tana taka muhimmiyar rawa wajen kasuwanci, mu’amala tsakanin jama’a, da kuma samun damar ayyukan zamani na dijital. Don haka idan network ya lalace, hakan na shafar aiki, kasuwanci, da kuma amincewar jama’a ga tsarin sadarwa.
Duk da cewa a baya NCC tana amfani da tarar kudi wajen hana kamfanoni yin sakaci, yanzu tana daukar wani sabon tsari da zai fi mayar da hankali kan kare hakkin masu amfani, domin kara gaskiya da daukar alhaki a cikin harkar.
Hukumar ta ce wannan mataki zai kara taimakawa kokarin da take yi na sa ido kan ingancin sadarwa da kuma tilasta bin ka’idojin aiki.
Bugu da kari, NCC ta kuma umurci Kamfanonin Hasumiyoyi da ke da muhimman kayan aiki kamar masts, su zuba jari a kayan more rayuwa domin inganta network, ta hanyar amfani da kudaden da NCC ta taba ci tarar su, tare da karin tarar da hukuma za ta iya kakaba musu.
NCC ta ce za ta ci gaba da matsa wa kamfanonin sadarwa lamba su rika zuba jari a karfafa network, fadada karfin aiki, da inganta kayan more rayuwa domin biyan bukatar jama’a da ke kara yawa.
Haka kuma za ta ci gaba da amfani da dokoki da matakai da za su tabbatar da adalci, gaskiya, da daukar alhaki, domin tabbatar da cewa kowane dan Najeriya ya samu ingantaccen network kamar yadda ya dace, tare da gina ingantacciyar masana’antar sadarwa da za ta taimaka wajen bunkasa Najeriya a fannin dijital.