NEMA takarbi yan Nigeria da suka dawo daga jamhoriyar nijar da suka sauka a filin jirgin sama na malam aminu kano dake kano
Shugaba sashin ayyuka na hukumar NEMA rashen jahar Kano, Dr. Nura Abdullahi, ya ce komawar ta kasance ta son rai, ba tilastawa ba, kuma Gwamnatin Tarayya ce ta dawo da su ta Ma’aikatar Harkokin Waje.
Ya ce adadin wadanda suka dawo sun hada da manyan maza 267, manyan mata 101, yara maza 82 da yara mata 72, daga jihohi kamar Kano, Jigawa, Plateau da Bauchi.
NEMA tare da sauran hukumomi sun shirya domin kula da su, inda aka ba su abinci, bargo, gidan sauro da kayan tsafta, sannan za a tura su zuwa jihohinsu bayan kammala rajista.