An ɗage sauraron bada beli na El-Rufai zuwa Laraba yayin da aka tsaurara tsaro a babbar tarayya Kotun tarayya dake Kaduna
Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar beli da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, zuwa ranar Laraba.
Mai shari’a Justice Rilwanu ne ya sanya sabon ranar bayan sauraron hujjojin ɓangaren lauyan kare El-Rufai da kuma na masu gabatar da ƙara.
Hukumar ICPC ce ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu kan tuhuma 10, waɗanda suka haɗa da zargin mayar da kadarorin gwamnati mallakar kai da kuma halasta kuɗaɗen haram El-Rufai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka gabatar masa.
A wani shari’ar daban, El-Rufai ya kuma bayyana a gaban Kotun Jiha ta Kaduna (Kaduna State High Court) bisa zargin:
cin zarafin ofis,
damfara,da yunƙurin aikata damfara.
ICPC ta shigar da ƙarar mai lamba KDH/KAD/ICPC/01/26 a kan El-Rufai tare da wani mutum mai suna Amadu Sule, wanda ke aiki a Hukumar Bunƙasa ta Jihar Kaduna (LEDA).
Rahoton daga kafar yada labarai ta kasa (NAN) ya ce El-Rufai ya isa harabar Kotun Tarayya da misalin ƙarfe 9:40 na safe, yana tare da jami’an ICPC.
An kuma tsaurara tsaro a faɗin birnin Kaduna kafin zaman kotun, inda aka jibge jami’an tsaro masu ɗauke da makamai daga:
‘Yan sanda,
DSS,
da Kaduna State Vigilance Service,
a muhimman wurare.
An takaita shiga kotun ga ‘yan jarida masu katin shaida da jami’an kotu kaɗai, amma an hana ‘yan jarida shiga cikin ɗakin kotu domin ɗaukar rahoto kai tsaye.
Lauyan El-Rufai, Abdul Adamu, ya ƙi yin cikakken bayani bayan zaman, sai dai ya ce an ɗage shari’ar zuwa gobe.