Rundunar. Yan Sandan jahar edo Sun Kama Mutane 65 da Ake Zargi da Garkuwa da Mutane, Sun kuma Kwato Naira Miliyan 1.8

Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo. ta kama mutane 65 da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane, tare da kwato kudi har Naira miliyan 1,850,000 da ake zargin kudin fansa ne, a yankin Aviele.

 

 

 

 

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Eno Ikoedem, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, 6 ga Maris, 2026.

 

 

 

 

 

Ta ce rundunar ta samu gagarumar nasara ne bayan wani samame na tsakar dare da aka kai ranar 2 ga Maris, 2026, da misalin karfe 2:45 na dare.

 

 

 

 

 

A cewarta, bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ana ganin wasu da ake zargi da garkuwa da mutane a wani Zango da kuma wani wuri mai suna Max Square Properties a Aviele, tare da wasu bayanan fasaha da suka nuna cewa ana tattaunawar neman kudin fansa daga yankin, jami’an rundunar na hedikwatar jihar tare da hadin gwiwar jami’ai daga ofisoshin Auchi da Ekpoma suka kai farmaki wuraren.

 

 

 

 

Samamen ya kai ga kama mutane 65 da ake zargi, tare da kwato kayayyaki da dama da suka hada da kudin Naira miliyan 1,850,000 da ake zargin kudin fansa ne, da kuma kayan sanye da kayan  sojojin Nigerian Army da wasu kayayyaki masu alaka da aikata laifi.

 

 

 

 

Sanarwar ta ce babu wanda ya rasa ransa yayin aikin.

 

 

An garzaya da wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sanda a Benin City domin ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan rawar da kowannensu ya taka a laifukan garkuwa da mutane.

 

 

 

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Agbonika, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa kwarewa, tare da jaddada kudurin rundunar na ci gaba da rusa kungiyoyin masu garkuwa da mutane a fadin jihar.

 

 

Ya kuma bukaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai da bayanai.

You might also like
Leave a comment