Yunkurin tsige mataimakin gwamna. kungiyar kwankwasiya ta mai da martani kan Almundahanar biliyan 1.1 da akewa mataimakin gwamnan
Kungiyar darikar siyasar Kwankwasiyya a Jihar Kano ta mayar da martani kan zargin almundahanar Naira biliyan 1.1 da ake yi wa Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, inda ta ce tana da takardu da ke nuna cewa an fitar da kudin ne da amincewar gwamna, Abba Kabir Yusuf.
A ranar Alhamis ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta mika wa mataimakin gwamnan takardar sanarwar tsige shi daga mukaminsa, bisa zargin aikata manyan laifuka,
amfani da ofis ba bisa ka,Ida ba, da kuma cin amana.
Takardar tsige shi da ‘yan majalisa 38 cikin 40 suka sanya wa hannu, ta zargi Gwarzo da rashin gaskiya a harkokin kudi tun lokacin da yake Kwamishinan Kananan Hukumomi, har zuwa lokacin da yake Mataimakin Gwamna.
Sai dai wasu takardu daga watan Afrilu zuwa Yuni na shekarar 2024 da kungiyar Kwankwasiyya ta fitar sun nuna wani sabon bayani daban.
Takardun sun nuna cewa an amince da ware Naira biliyan 1.1 domin samar da ruwa da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar, kuma an yi hakan ne da sahalewar gwamnan.
A ranar 15 ga Afrilu, 2024, kungiyar Association of Local Governments of Nigeria reshen Kano ta rubuta wa Ma’aikatar Kananan Hukumomi takarda tana neman kudin domin magance karancin ruwa da kuma samar da magunguna.
An nuna cewa Mataimakin Gwamna ya goyi bayan bukatar kafin daga bisani a mika ta ga gwamna.
A cikin wata takarda da aka aikawa gwamnan, an bayyana cewa shugabannin kwamitocin rikon kananan hukumomi 44 karkashin ALGON sun ba da shawarar a ware Naira miliyan 25 ga kowace karamar hukuma daga asusun hadin gwiwar jiha da kananan hukumomi, wanda jimillarsa ya kai Naira biliyan 1.1.
Daga baya, a ranar 14 ga Mayu 2024, Mataimakin Gwamnan ya rubuta takarda yana neman amincewar gwamnan domin a fitar da kudin, inda ya ce hakan zai taimaka wajen magance matsalar karancin ruwan sha a kananan hukumomi 44, tare da tallafawa marasa karfi wajen samun ingantattun magunguna.
A karshe, a ranar 10 ga Yuni 2024, an bayar da amincewar fitar da kudin a wata takarda da Abubakar S. Dabo ya sanya wa hannu a madadin kwamishina.
An kuma bayyana yadda aka raba kudin kamar haka:
Naira miliyan 10 ga kowace karamar hukuma domin gyara rijiyoyi da burtsatse.
Naira miliyan 15 ga kowace karamar hukuma domin samar da magunguna da kayan asibiti.
Wannan ya kai Naira miliyan 25 ga kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 44, wanda jimillarsa ta kai Naira biliyan 1.1.
Shugabannin Kwankwasiyya sun ce wadannan takardu sun tabbatar da cewa Mataimakin Gwamnan ya yi abin da ya dace bisa doka kuma da cikakkiyar amincewar gwamnan, suna mai cewa zargin da majalisar ta yi masa na da alaka da siyasa.
Lamarin tsige shi ya zo ne a lokacin da ake fuskantar tsananin takun-saka na siyasa a Kano, musamman bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party zuwa All Progressives Congress.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa yunkurin tsige Gwarzo na da nasaba da doka da kuma siyasa, musamman bayan da ya ki sauya sheka tare da gwamnan zuwa APC, ya kuma zabi ci gaba da kasancewa a NNPP/Kwankwasiyya.
An bai wa Mataimakin Gwamnan wa’adin makonni biyu domin ya mayar da martani kan zargin da ake masa.
Idan majalisar ba ta gamsu da bayaninsa ba, ana sa ran za ta kafa kwamitin bincike kamar yadda sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya tanada.
Yunkurin jin ta bakin gwamnatin jihar bai yi nasara ba, domin Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi alkawarin dawowa da bayani amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai yi hakan ba. Daily Trust