Shettima ya dawo Najeriya bayan halartar taron tattalin arziki na duniya

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya koma Abuja bayan balaguron da ya yi inda ya shafe mako guda yana gudanar da harkokin diflomasiyya da tattalin arziki a ƙasashen Guinea-Conakry da Switzerland.

 

Wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai Stanley Nkwocha ya fitar ta ce mataimakin shugaban ƙasar ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe ranar Asabar.

 

Ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wajen bikin rantsar da shugaban ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, ya kuma jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron tattalin arziki na duniya (WEF) karo na 56 a Davos.

 

Da farko dai Shettima ya ziyarci birnin Conakry, inda ya halarci bikin rantsar da shugaba Doumbouya, inda ya jaddada rawar da Najeriya ke takawa a cikin ƙungiyar ECOWAS da kuma buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannin noma da masana’antu.

 

A cewar mataimakin shugaban ƙasar, wannan tafiya ta nuna yadda gwamnatin Najeriya ta ƙara ƙaimi wurin tabbatar da haɗin kan yankin yammacin Afirka da kuma ƙudurin da ta ɗauka na sake farfado da tattalin arzikin ƙasa ƙarƙashin shugaba Tinubu.

You might also like
Leave a comment