Sojoji sun sha alwashin kuɓutar da masu ibada da aka sace a kaduna

Rundunar sojin Najeriya ta musanta iƙirarin cewa ta yi tafiyar hawainiya wurin kai ɗauki lokacin da aka kai hari a yankin Kurmin Wali da ke jihar Kaduna, inda aka sace masu ibada sama da 100 a ranar Lahadin da ta gabata.

 

Wasu daga cikin al’ummar da ke ƙaramar hukumar Kajuru, sun yi zargin cewa sojojin sun yi ƙasa a gwiwa, inda suka yi zargin cewa jami’an tsaro ba su yi gaggawar kuɓutar da masu ibadar da aka sace ba.

 

Sai dai shalkwatar tsaron ƙasar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su cikin gaggawa.

 

A cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar, ya bai wa al’ummar tabbacin ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.

 

“Saɓanin iƙirari cewa an yi ƙasa a gwiwa wurin kuɓutar da waɗanda aka sace,Rundunar sojin ƙasa, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, suna ci gaba da aiwatar da ayyukan leƙen asiri a yankin dazukan da ƴan bindigar ke ciki,” in ji sanarwar.

 

Rundunar ta kuma jaddada aniyar ta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda ta sha alwashin sake haɗa waɗanda harin na Kurmin Wali ya rutsa da su da iyalansu.

 

You might also like
Leave a comment