Shohuwar ministan manfetur ta nigeria diezani ta baiyana agaban kotu a london
Tsohuwar ministar harkokin man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, ta bayyana a gaban Kotun Southwark Crown da ke birnin Landan, kan shari’ar da ake yi mata na tuhumar cin hanci na fam 100,000 kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Alison-Madueke, wadda ta riƙe mukamin minista daga shekarar 2010 zuwa 2015, ita ce mace ta farko da ta rike mukamin ministar man fetur a Najeriya kuma ita ce mace ta farko da ta shugabanci ƙungiyar mai ta duniya, OPEC..
An gurfanar da Diezani kan laifuka guda shida da ta musanta, bayan da hukumar NCA ta Birtaniya ta tuhume ta a shekarar 2023 da karɓar cin hanci daga 2011 zuwa 2015.
Tuhume-tuhumen sun haɗa da cin hanci na aƙalla fam 100,000 da mallakar motoci masu direba da jiragen sama masu zaman kansu, da amfani da gidaje da yawa a London ba bisa ƙa’ida ba da sauransu.
An tsara fara shari’ar a ranar Litinin, 26 ga Janairun 2026, wadda ake sa ran za ta ɗauki makonni 10 zuwa 12.