Sojoji Sun Kashe Shugaban ‘Yan Ta’adda Munzir, Sun Kama Wasu 34 A Borno
Hedkwatar Tsaro (DHQ) ta ce sojoji sun kashe wani kwamandan ‘yan ta’adda, Munzir (wanda aka fi sani da Baa Yanziye), tare da wasu da dama a lokacin hare-haren sama da kuma kama ‘yan ta’adda 34 a cikin makonni biyu da suka gabata a yankin Arewa maso Gabas.
Daraktan Ayyukan Watsa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce wani kwamandan ‘yan ta’adda mai suna Yakubu Adamu ya mika wuya ga sojoji da makamansa da harsasai a yankin Azir Wajiroko.
Ya ce sojoji tsakanin 1 ga Janairu zuwa 15, 2026, sun gudanar da ayyuka kan ‘yan ta’adda a kananan hukumomin Gwoza, Konduga, Bama da Damboa na Jihar Borno.
Har ila yau, sojojin sun kuma ci gaba da kai samame a sauran yankunan da suka hada da Askira Uba, Chibok, Mafa da Guzamala a jihar.
Ya kara da cewa, sojoji a lokacin fafatawar sun kashe ‘yan ta’adda da dama, sun kama 34 sannan sun ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su.