Shugaba Tinubu Zai bar nigeria a gobe Litinin Zuwa Ziyarar Aiki kasar Turkiyya
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja ranar Litinin zuwa ziyarar aiki a ƙasar Turkiyya, domin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da faɗaɗa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce ziyarar za ta mayar da hankali ne kan ƙara ƙarfafa kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin ƙasashen biyu tare da binciko sabbin fannoni na haɗin gwiwa.
A cewar sanarwar, manyan batutuwan da za amai da hankali wajen tattaunawar siyasa da diflomasiyya sun haɗa da tsaro, ilimi, ci gaban al’umma, kirkire-kirkire, harkar jiragen sama, kuɗi da bankuna, sadarwa, kasuwanci da zuba jari.
Onanuga ya ƙara da cewa Najeriya da Turkiyya za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyi (MoU) da dama da suka shafi binciken kimiyya, makamashi, haɗin gwiwar fasaha, kafofin watsa labarai da sadarwa, haɗin gwiwar soja, da kuma ladabi na diflomasiyya.
Ya kuma bayyana cewa za a shirya taron kasuwanci a lokacin ziyarar, domin haɗa ’yan kasuwa da masu zuba jari daga ƙasashen biyu don tattauna damarmmakin da za su amfanar da juna.
Wannan ziyara ita ce ta farko da Shugaba Tinubu zai kai ƙasar Turkiyya tun bayan hawansa mulki. Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, ya kai ziyara Najeriya a watan Oktoban 2021.
Shugaba Tinubu zai tafi tare da manyan jami’ai, ciki har da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar; Antoni Janar na TTarayyada kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi; Ministan Tsaro, Christopher Musa; da Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Jimi Benson.