Wata Guguwa tayi sanadiyar katsewar wutar lantarki a wasu sassan Amurka
Aƙalla gidaje da shaguna 600 ne suka rasa wutar lantarki a Amurka sakamakon wata mummunar guguwa da ta auka wa ƙasar.
Jihohin kudancin ƙasar, irin su Tennessee da Texas da Mississippi a kuma Louisiana ne lamarin ya fi ƙamari.
Al’ummar ƙasar da dama ne suka fuskanci wannan guguwa, yayin da ake fama da tsananin sanyi inda a wasu biranen yake maki 20 ƙasa da sufuli a ma’aunin salshiyos.
Hukumar kula da hasashen yanayi ta ƙasar ta yi gargaɗin samun mummunar iska da saukar dusar ƙanƙara mai yawa a wasu sassan New England.