Zargin Juyin Mulki: wata Ƙungiya Ta Nemi A Saki Jami’an Soja da Aka Tsare Saboda Matsalolin Lafiya

Wata ƙungiya mai suna Concerned Pro-Democratic Activists of Nigeria ta roƙi gwamnatin tarayya da ta saki jami’an soja da aka tsare bisa zargin yunƙurin juyin mulki a watan Oktoban bara, har sai an kammala bincike kan lamarin.

 

 

Shugaban ƙungiyar, Kwamared Yusuf Musa Dauda  shine ya yi wannan roƙo a yayin taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

 

 

Ya bayyana damuwarsa cewa wasu daga cikin jami’an da aka kama tun watan Oktoban bara suna fama da munanan cututtuka a cikin tsarewa, ba tare da samun kulawar lafiya yadda ya kamata ba.

 

 

Kwamared Yusuf Musa Dauda ya kuma koka da yadda aka hana iyalan jami’an damar ganinsu ko yin magana da su tun lokacin da aka kama su, domin su san halin da suke ciki kuma su samu kwanciyar hankali.

 

 

 

Ƙungiyar ta nuna damuwa kan tsawaita tsare jami’an ba tare da shari’a ko bin ka’idojin doka ba a cikin “zamanin dimokuraɗiyya”, tare da roƙon Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani domin a sake su idan babu wata shari’a tabbatacciya a kansu.
Ya ce:

 

 

 

“Rundunar Tsaron Najeriya, ta hannun tsohon Daraktan Bayanin Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, a ranar 4 ga Oktoba 2025, ta sanar da kama wasu jami’an soja bisa zargin rashin da’a da karya dokokin aiki.
“Sojojin sun ce bincike ya nuna cewa koke-koken jami’an da aka kama na da alaƙa da yawan faɗuwa jarrabawar ƙarin girma da kuma jin cewa aikinsu ya tsaya cik.

 

 

“Bayan wasu makonni, sai jita-jita suka bazu cewa kamun nasu ya shafi zargin yunƙurin juyin mulki, amma nan take sojoji da gwamnati suka ƙaryata hakan.
“Duk da cewa muna matuƙar Allah-wadai da duk wani yunƙurin kifar da gwamnati ta hanyar da ba ta dimokuraɗiyya ba, muna so mu ja hankalin jama’a da hukumomi da su duba wannan lamari da adalci.

 

“Saboda haka, muna roƙon gwamnatin tarayya, shugabanninmu, da hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an ba jami’an kulawar lafiya yadda ya kamata.”

 

 

Ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta ba jami’an da aka tsare dama su riƙa sadarwa da iyalansu, domin rage musu damuwa da tabbatar musu da cewa suna cikin koshin lafiya.

You might also like
Leave a comment