Shugaban kasa bola Ahmad tunibu yace gwamnatinsa Za ta kawar da barazanar ƴanbindiga a Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta magance barazanar da ƴanbindiga da ƴan fashin daji ke yi wa ƙasar.

 

 

 

 

 

Yayin da yake jawabi a taron majalisar zartaswa ta kasa da ke gudana a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce za mu ƙara ƙoƙari domin lalubo hanyoyin ƙarfafa jami’an tsaronmu domin kawar da ayyukan ta’adanci da na ƴan fashin daji.

 

 

 

 

 

“Wannan ce matsalar da ke hana mu barci, amma na tabbatar muku cewa ina da ƙwarin gwiwa za mu yi nasara a kan su, mu kawar da ayyukansu, wannan baƙon al’amari ne, ba al’adarmu ba ce,” in ji shi.

 

 

 

 

Haka kuma Shugaba Tinubu ya yaba wa wasu gwamnonin ƙasar, musamman na jihohin Borno da Katsina da Kaduna kan ƙoƙarin da ya ce sun yi wajen kare ƴanci da tsaron ƙasar

You might also like
Leave a comment