Tsohon gwamnan kaduna nasiru el,rufa,i ya musanta zargin Dangantaka ta Ƙashin Kai da shugaban Tinubu
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Malam Nasir El-Rufai, ya musanta rade-radin cewa akwai wata matsalar dangantaka ta ƙashin kai tsakaninsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa tun da farko ma ba su taɓa samun irin wannan dangantaka ba.
Da yake magana a wata hira da Trust TV a ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana cewa goyon bayan da ya bai wa takarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya samo asali ne daga biyayya ga jam’iyya da kuma lissafin siyasa, ba wai saboda wata abota ta musamman ba.
El-Rufai ya ce shigarsa cikin tafiyar da ta kai ga fitowar Tinubu a matsayin ɗan takarar APC ta biyo bayan shawarwari ne a cikin jam’iyyar da kuma la’akari da yanayin siyasar ƙasa kafin zaɓe.
“Wasu shugabannin Musulmi daga Kudu maso Yamma ne suka tuntube ni domin in mara wa ɗan takarar Musulmi daga yankin Daga nan ne tattaunawar ta fara,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa tsarin rabon mulki (zoning) a cikin APC bayan wa’adin shekaru takwas na Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya komawar mulki zuwa Kudu ta zama dole.
“A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC kuma Gwamnan Kaduna a wancan lokaci, na san akwai fahimtar cewa bayan shekaru takwas na Buhari, mulki zai koma Kudu. Ba batun Tinubu ba ne kai tsaye; shi kawai ya amfana da yanayin,” in ji El-Rufai.
Ya bayyana cewa da zarar Tinubu ya samu tikitin takarar jam’iyya, ya jajirce wajen yaƙin neman zaɓe bisa ƙa’idarsa ta siyasa.
“Ƙa’ida ce a gare ni in yi iya ƙoƙarina domin ɗan takarar jam’iyyata a kowane zaɓe, ko da kuwa ina so ko ban so. Da ya zama ɗan takarar jam’iyya, dole ne in ba da dukkan ƙarfi na domin nasararsa,” ya faɗa.
Sai dai El-Rufai ya ce bayan zaɓe ne aka fara ganin bambance-bambancen fahimta, musamman a kan salon mulki da hidimar jama’a.
“Ba wai mun samu sabani ba ne; kawai ba mu samu wuraren da muke haɗuwa ba. Ni ina shiga gwamnati ne domin yi wa jama’a hidima da samar da sakamako, ba domin in tara dukiya ko naɗa na kusa da ni ba,” in ji shi.
A cewarsa, salon tafiyar da mulki na gwamnatin yanzu ya sha bamban da abin da ya yi imani da shi.
“Falsafar wannan gwamnati ta saɓa da duk abin da aka koya min a matsayin Musulmi, ɗan Arewa kuma ɗan Najeriya. Sun zo su raba ‘cake’ ne su wadata kansu. Mu mutane ne mabambanta — layuka ne da ba za su taɓa haɗuwa ba,
El-Rufai ya kuma bayyana cewa ƙin amincewa da tayin mukamin minista da Shugaba Tinubu ya yi masa ya samo asali ne daga irin waɗannan ƙa’idoji nasa.
“Da na amince da mukamin minista da aka sanar a bainar jama’a, da ba da daɗewa ba zan yi murabus. Falsafar mulkinmu ta yi nisa da juna ƙwarai,” in ji shi.