Majalissar dattijai ta amince da dokar zabe ta aika sako kai tsaye ta na,ura daga rufar zabe
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wani muhimmin sashe a cikin gyaran dokar zaɓe da ya wajabta aika sakamakon zaɓe kai tsaye ta na’ura daga rumfunan kaɗa ƙuri’a, domin jama’a su ga sakamakon ba tare da jinkiri ba.
Majalisar ta ce wannan hanyar ta na’ura ce za ta zama babbar hanya ta farko wajen isar da sakamako.
Sai dai dokar ta tanadi cewa idan aka samu matsalar intanet ko tangardar fasaha, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) za ta iya amfani da takardar rubutu a matsayin madadin.
Ƙudirin ya samu amincewa ne bayan Sanata Tahir Munguno ya gabatar da shi, tare da samun goyon bayan rinjayen sanatoci a zaman majalisar.
Bayan amincewa da ƙudirin, Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin mambobi 12 da zai yi aiki tare da Majalisar Wakilai domin daidaita dokar.
Masana siyasa da masu kare dimokuradiyya na kallon matakin a matsayin babban ci gaba da zai rage maguɗin zaɓe, ƙara gaskiya da kuma dawo da amincewar jama’a ga tsarin zaɓen Najeriya.