SHUGABA TINUBU YA NAƊA SHUGABA DA MEMBOBIN HUKUMAR NEMSA YA KUMA NAƊA MAGAJI DA’U ALIYU A MATSAYIN MD NA SHESTCO

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Hon. Magaji Da’u Aliyu a matsayin Manajan Darakta   na Sheda Science and Technology Complex (SHESTCO), Abuja.
SSHESTCO hukuma ce dake  da  alhakin gudanar da bincike da haɓaka fasaha (research and development) tare da kula da cibiyar binciken nukiliya.

 

 

 

Haka kuma, Shugaba Tinubu ya naɗa Engr. Adesayo Olusegun Michael a matsayin Manajan Darakta  Shugaban Hukumar Nigerian Electricity Management Services Agency (NEMSA).
Sauran mambobin Hukumar NEMSA da Shugaban Ƙasa ya naɗa sun haɗa da:
Engr. Aliyu Abdulazeez – Darakta na Zartarwa Ikechi Clara Nwosu – Shugaba (South East)
Zubair Abdur’rauf Idris – Mamba
Igba Elizabeth – Mamba (North Central)
Sani Alhaji Shehu – Mamba (North East)
Adeyemi Adetunji – Mamba (South West)
Engr. Emmanuel Eneji Nkpe – Mamba (South South)
Engr. Charles Ogbonna Asogwa – Mamba (South East)

 

 

 

Haka zalika, Shugaban Ƙasa ya naɗa Amina Gamawa, mai wakiltar Bauchi, da Abdullahi Muktar, mai wakiltar Kaduna, a matsayin Kwamishinoni na Hukumar Revenue Mobilisation Allocation and Fiscal Commission (RMAFC).

 

 

 

Shugaban Ƙasa ya aika sunayen waɗannan mutane biyu zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa.

 

sanarwa; Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara
(Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare)

Bayo Onanuga

10 ga Fabrairu, 2026

You might also like
Leave a comment