Tinubu zai gana da Sarki charles III a ranar laraba a birnin landon
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai gana da Sarki Charles III a yau ranar Laraba domin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da gano damar ƙarin zuba hannun jarin ƴan kasuwa.
Duk da cewa Tinubu ya ziyarci Britaniya sau da dama a lokacin mulkinsa, wannan ce ziyarar aiki ta farko tsakanin ƙasashen cikin kusan shekaru arba’in.
Shugaban da matarsa, Oluremi Tinubu, sun isa filin jirgin saman Stansted ranar Talata inda Sarki Charles zai karɓi Tinubu a gidan sarauta na tarihi na Windsor Castle kafin ya shirya liyafar ƙasa da ƙasa da yamma.
Birtaniya da Najeriya na da kyakkyawar alaƙa ta diflomasiyya, inda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniya ta haɗin kai a Nuwamba 2024 don ƙarfafa tattalin arziki da shige da fice da kuma tsaro.
Ziyarar Tinubu na zuwa ne bayan harin bam ɗin kunar bakin wake da ake zargi ya kashe aƙalla mutane 23 a Maiduguri ranar Litinin da yamma inda ya ba da umarnin tura manyan jami’an tsaro zuwa jihar don “ɗaukar ragamar al’amura.”
Najeriya dai ta kasance cikin rikicin masu iƙirarin jihadi tun a shekarar 2009.
An tsara cewa ranar Alhamis, Tinubu zai gana da Keir Starmer da ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje.