Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutu karamar sallah
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 19 ga Maris da Juma’a 20 ga Maris 2026 a matsayin ranakun hutu domin bikin Eid al-Fitr,
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya bayyana hakan a madadin gwamnati, inda ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumi cikin nasara.
A cikin sanarwar da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar, an bukaci Musulmi da su ci gaba da riko da darussan da aka koya a watan Ramadan kamar soyayya, kyautatawa, haƙuri, zaman lafiya da sadaukarwa.
Har ila yau, gwamnati ta bukaci daukacin ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Gwamnatin ta kuma shawarci jama’a da su yi bikin Sallah cikin natsuwa, tare da taimaka wa marasa galihu, domin ƙarfafa zumunci da jinƙai a cikin al’umma.