Gwamnatin jahar Kano Ta Fitar da Sabbin Bayanan kan Rikicin. Hawan sallah “Sarakuna Biyu”

Shirin gudanar da Hawan Sallah  a Kano ya sake jawo hankalin jama’a, sakamakon rikicin sarauta da ke tsakanin bangarori biyu, inda ake samun sabani kan wanda zai jagoranci bikin.

 

 

 

 

 

 

Mai ba gwamna shawara kan harkokin masarautu, Farfesa Tijjani Muhammad Naniya, ya bayyana cewa Muhammadu Sanusi II shi ne halastaccen Sarkin Kano,

 

 

 

 

 

kuma shi ne zai jagoranci Hawan Sallah.
Sai dai kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa har yanzu batun yana gaban kotu, yana mai gargadin kada a fitar da bayanan da za su iya rikita jama’a.

 

 

 

 

 

 

A gefe guda kuma, Aminu Ado Bayero ya sanar da jami’an tsaro cewa zai gudanar da nasa Hawan Sallah daga fadarsa da ke Nassarawa, yayin da magoya bayansa ke cewa sun riga sun fara shirye-shirye.

 

 

 

 

 

indai ba ,amanta  Rikicin ya samo asali tun shekarar 2019 lokacin da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya raba masarautar Kano zuwa gida biyar, lamarin da ya rage ikon Muhammadu Sanusi II. A 2020 kuma aka sauke shi daga sarauta, aka nada Aminu Ado Bayero a matsayin sarki.

 

 

 

 

 

 

A shekarar 2024, gwamna Abba Kabir Yusuf ya soke dokar da ta kirkiri sabbin masarautu tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki. Duk da haka, Aminu Ado Bayero ya ci gaba da ikirarin shi ne halastaccen sarki daga fadarsa ta Nassarawa.

 

 

 

 

 

 

Wannan rikici ya jawo gudanar da bukukuwa daban-daban a baya, ciki har da Sallar Idi da Hawan Sallah na daban-daban a shekarun baya.

 

 

 

 

Yanzu haka, yayin da ake shirin Hawan Sallah na 2026, akwai fargabar cewa za a iya samun bukukuwa biyu a lokaci guda idan ba a samu matsaya daga kotu ba.

 

 

 

 

 

 

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa kotu ce kadai za ta warware wannan rikici, yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da tsayawa kan matsayinsu.

You might also like
Leave a comment