Sarkin Musulmi Ya Bukaci Afara duba watan Sallah Ranar Laraba
Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci al’ummar Musulmi a fadin Najeriya da su fara neman ganin jinjirin watan Shawwal da zai nuna karshen azumin watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa da Majalisar Masarautar Sakkwato ta fitar, wadda Sambo Wali Junaidu ya sanya wa hannu, an bayyana cewa ranar Laraba, 18 ga Maris 2026 (29 ga Ramadan 1447AH), ita ce ranar da za a nemi jinjirin watan.
Sanarwar ta ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da hakimin yankinsa ko shugaban ƙauye, domin su mika rahoton ga Masarautar Sakkwato domin tabbatarwa.
Haka kuma, an bayar da lambobin waya domin sauƙaƙa isar da sahihin rahoton ganin wata kai tsaye zuwa ofishin Sarkin Musulmi.
Ganin jinjirin watan Shawwal ne ke nuna ƙarshen azumi da kuma shigowar bikin Eid al-Fitr.
Kamar yadda aka saba, Sarkin Musulmi shi ne ke sanar da ranar Sallah a hukumance bayan an tabbatar da ganin wata daga sassa daban-daban na ƙasar.