Shugaban kasa bola Tinubu Ya Umurci Shugabannin Tsaro Su Koma Maiduguri
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci shugabannin hukumomin tsaro da su koma birnin Maiduguri domin su jagoranci shawo kan matsalar tsaro a yankin.
Wannan mataki na zuwa ne bayan hare-haren bama-bamai da dama da suka yi sanadin mutuwar fiye da mutane 20 tare da jikkata sama da 100 a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai hare-haren a lokaci guda da misalin karfe 7:25 na yammacin ranar Litinin.
A martaninsa kafin ya tafi wata ziyarar aiki zuwa United Kingdom, Tinubu ya ce Najeriya ba za ta tsorata ba sakamakon irin wadannan hare-hare.
Ya kuma bayyana cewa:
Ya yi jimamin wadanda suka rasa rayukansu
Ya jajanta wa wadanda suka jikkata
Kuma ya nuna goyon baya ga al’ummar Borno
Shugaban ƙasar ya kara da cewa hare-haren na baya-bayan nan alamu ne na ƙoƙarin ƙarshe na ‘yan ta’adda domin tsoratar da jama’a, yana mai jaddada cewa sojoji da jami’an tsaro na ci gaba da matsa musu lamba.
Tinubu ya kuma yaba wa jarumtar sojojin Najeriya da suka dakile wasu hare-haren da aka kai kan sansanonin soja, tare da tabbatar da cewa:
Za a ƙara ƙarfafa yaƙi da ta’addanci
An kuma amince da ƙarin kayan aiki da tallafi ga jami’an tsaro
Hukumomin agaji za su kula da waɗanda suka jikkata
A ƙarshe, ya jaddada cewa babu wani wuri a Najeriya da ‘yan ta’adda za su samu mafaka, yana mai cewa za a gano su, a tunkare su, kuma a kawar da su gaba ɗaya.