An Kama wani Jami’in Sojin Sama na Najeriya Kan zargin Harbin wani mutum da Ya Yi Sanadin Mutuwarsa a Port Harcourt

An kama wani jami’in Sojin Sama na Najeriya (NAF) bayan ya harbe wani mutum har lahira a unguwar   Harmony Estate da ke kan titin Eliozu a birnin Port Harcourt, Jihar Rivers.

 

 

 

 

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Asabar, 14 ga watan Maris, kamar yadda wani kafar yada labarai ta Zagazola Makama, mai mayar da hankali kan harkokin yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ta bayyana.

 

 

 

 

 

 

Majiyoyi sun ce jami’in, mai suna Oton Uba Eli, wanda ke aiki da rundunar 115 Special Operations Group, ya tsare wani mai aikin  kai sakonni mai shekaru 28, mai suna David Ebuka, bisa zargin mallakar wasu kwayoyi masu hadari.

 

 

 

 

A yayin da ake cikin wannan yanayi, wani mutum da ake zargin shi ne shugaban Ebuka, mai suna Joseph Iche Johnson, ya isa wurin, lamarin da ya janyo gardama a tsakaninsu. A cikin wannan takaddama, jami’in Sojin Saman ya harba bindigarsa, inda harsashin ya samu Johnson, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

 

 

 

 

 

 

 

An garzaya da wanda aka harba zuwa asibitin sojoji, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. Daga bisani, an kai gawarsa dakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Port Harcourt domin gudanar da binciken gawar.

You might also like
Leave a comment