Gwamnan kano Abba kabir yusuf ya amince da rushe ma,aikatar ilimi mai zurfi (ministry of higher education) tare da hadata da ma,aikatar ilimi (ministry of education) domin karfafa tsarin gudarwa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.
Yadda sabon tsarin zai kasance
Bayan wannan gyara:
Sabuwar ma’aikatar za ta kasance Ma’aikatar Ilimi.
Za a ƙirƙiri Sashen Ilimi Mai Zurfi (Directorate of Higher Education) a cikin ma’aikatar domin kula da harkokin manyan makarantu.
An bayyana sashen a wani bangare da famanan Sakatare (Permanent Secretary) ne zai jagorance shi.
Za a samar da ma’aikata da kayan aiki domin kula da jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare a jihar.
Canjin da zai shafi hukumomi
A karkashin sabon tsarin:
Hukumar Scholarship Board da sauran hukumomin da ke ƙarƙashin tsohuwar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi za su koma ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi.
Jami’o’in gwamnati da sauran manyan cibiyoyin ilimi na jihar za su kasance ƙarƙashin sabon Directorate of Higher Education.
Dalilin yin gyaran
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gyaran tsarin ilimi da ake yi domin: rage maimaita ayyuka tsakanin ma’aikatu
inganta haɗin kai a manufofin ilimi
rage kuɗin gudanar da gwamnati
ƙara inganci da ɗaukar alhaki a tafiyar da ilimi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manyan gyare-gyare domin farfaɗo da ɓangaren ilimi da kuma samar wa matasa makoma mai kyau.
A ƙarshe, ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar da kuma Shugaban Ma’aikatan Jihar an umarce su da su tabbatar da cewa an aiwatar da wannan sauyi cikin gaggawa ba tare da tangarda ba.