Wasu da ake zargin yan daba ne sun tarwatsa taron jam,iyyar ADC a jahar River

Rundunar ‘yan sanda ta jihar river  ta bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan daba ne na siyasa  sun  kai hari tare da tarwatsa taron jam’iyyar.

 

 

 

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Sunday Eitokpah, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi yayin da yake martani kan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta wanda ke nuna yadda aka tarwatsa taron jam’iyyar.

 

 

 

 

A cikin bidiyon da ya karade intanet, an ji wani daga cikin ‘yan daban yana umartar sauran su tarwatsa komai, yana cewa jam’iyyar African Democratic Congress ba ta nan lokacin da All Progressives Congress ke aikin gyara da ci gaban yankin majalisar.

 

 

 

 

 

Kakakin ‘yan sandan ya ce taron, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, bai ma fara ba tukuna lokacin da wasu bata-gari suka bayyana ba zato ba tsammani suka lalata kayan taron.

 

 

 

 

inda yace.  Lokacin da ake shirin fara taron ne waɗannan bata-gari suka fito daga inda ba a sani ba suka tarwatsa rumfuna   kujeru da kuma kayan sauti.”

 

 

Sai dai ya tabbatar da cewa jami’an tsaro da tawagar musamman sun isa wurin domin dakile rikicin kada ya rikide zuwa babban tashin hankali.

 

 

 

 

 

A cewarsa, saboda yanayin tashin hankali da rudanin da ya faru, ba a kama kowa ba zuwa yanzu, kuma taron bai samu damar ci gaba ba.

 

 

 

 

Rahotanni sun kuma nuna cewa makamancin wannan lamari ya faru a ranar Talata a garin Calabar, inda aka tarwatsa wani taron jam’iyyar.

 

 

 

 

Jam’iyyar African Democratic Congress ta yi tir da lamarin, tana zargin cewa ana ƙoƙarin ƙwace tsarin jam’iyyar a jihar.

You might also like
Leave a comment