Tsohon shugaban jam,iyyar Apc Abdullahi umar ganduje A shirye nake na shirya da Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a shirye yake ya shirya da babban abokin siyasarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

 

 

 

Ganduje ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da BBC.

 

 

 

Ya ce, “Ina fatan nan gaba za mu daidaita da Kwankwaso, a tafi ga baki ɗaya domin harka ce ta siyasa. Da munyi siyasa tare da shi, mu ‘yan uwan juna ne.”

 

 

 

 

Ganduje da Kwankwaso dai sun jima ba sa ga maciji da juna a harkokin siyasar jihar Kano, kuma ana ganin komawar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi zuwa jam’iyyar APC zai sake ruruta ƙiyayyar da ke tsakaninsu.

 

 

Ganduje ya ce abin da yanzu ya fi muhimmanci shi ne ci gaban al’ummar Kano da kuma nasarar jam’iyyar APC.

 

 

 

“Da anyi hamayya, yanzu ana tare. Wance shafi na hamayya an riga an rufe shi. Abin da aka sa a gaba shine ci gaban al’ummar Kano da samun nasara a wannan jam’iyya,” in ji shi.

 

 

 

Ya kara da cewa, “Idan Abba ya samu nasara, mun samu; in mun samu nasara, ya samu; idan ya faɗi, mun fadi; idan mun fadi, ya fadi. Duk wanda ya gane wannan, magana ce ta mu taimaka wannan gwamnati tayi nasara.”

 

 

Ganduje ya bayyana cewa kasancewarsa tsohon shugaban jam’iyyar APC na tsawon shekara biyu ya ba shi damar fahimtar tsarin jam’iyya da yadda ake tafiyar da al’amuranta.

 

 

 

 

“A kan batun ko za a ba Abba dama ya tsaya takara a jam’iyyar, na san abun da yaka a tsarin mulki da kuma abin da yake na al’ada na jam’iyyar. Al’ada ta jam’iyyar APC shine wanda yake gwamna, shi za a fara ba shi tayi idan yana sha’awa ya tsaya takara domin ya maimaita ko yayi tazarce, amma ba yana nufin duk sauran muƙame haka bane,” Ganduje ya ƙara da cewa.

 

 

 

Ganduje ya jaddada cewa hadin kai tsakanin shugabannin jam’iyya da ‘yan siyasa zai taimaka wajen samun nasara a jihar

← Back

Thank you for your response. ✨

You might also like
Leave a comment