Kalubalen Cin Zarafin kananan Yara a jahar Kano: Ana Amfani da Su wajen Sayar da Magungunan Gargajiya a Tituna
Al umma sun fara nuna damuwa matuƙa a Jihar Kano sakamakon yadda ake ci gaba da amfani da ƙananan yara wajen sayar da magungunan gargajiya a tituna da kasuwanni, lamarin da ke haifar da barazana ga ilimi, tsaro da lafiyar jama’a.
Rahotanni da shaidun gani da ido a wasu sassan birnin Kano sun nuna yadda yara ƙanana, wasu ma ‘yan shekarun firamare, na yawo da kekunan talla dauke da lasifika, suna tallata magungunan gargajiya iri daban daban..
Ana Zargin wannan Tsarine na Cin Zarafi
Bincike ya nuna cewa abin da ake gani kamar sana’ar talla ce ko wai taimakon iyaye kawai ba ne, sai dai ana zargin cewa akwai manya da ke daukar yaran aiki, suna basu kayan sayarwa tare da turasu zuwa yankuna daban-daban domin gudanar da tallace-tallace.
Ana kuma zargin cewa a ƙarshen rana, yara na mika kuɗin da suka tara ga waɗanda ke kula da su, yayin da su kuma ake basu ƙananan kuɗaɗe kaɗan a matsayin lada.
Masu sharhi sun bayyana cewa wannan tsari na iya zama wata hanyar cin gajiyar talauci da rashin kariyar yara, inda manya ke samun riba mai yawa, yayin da yara ke fuskantar wahala da haɗari.
Barazanar Ilimi da Makomar Yara
Masana harkar tarbiyya sun nuna cewa wannan dabi’a na iya janyo matsala mai girma, domin yara da dama suna shafe mafi yawan lokacinsu a titi maimakon zuwa makaranta.
Rahoton ya kuma nuna cewa yawan yawo a tituna na iya jefa yaran cikin haɗarin, cin zarafi, gurɓacewar muhalli da lalacewar tarbiyya.
Baya ga batun cin zarafin yara, an kuma bayyana damuwa kan irin magungunan da ake sayarwa, inda ake zargin cewa da dama daga cikinsu ba su da cikakken bincike ko sahalewar hukuma.
Haka kuma ana yawan tallata magungunan da ikirarin cewa suna warkar da cututtuka daban-daban ba tare da tabbacin likitanci ba, abin da zai iya jefa lafiyar jama’a cikin hatsari.
Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnatin Kano da hukumomin da abin ya shafa su dauki matakin gaggawa domin dakile wannan lamari.
Haka kuma akwai bukatar Ma’aikatar Harkokin Mata da Cigaban Al’umma ta ceto yaran tare da shirin gyara rayuwarsu.
Sannan Ma’aikatar Ilimi ta tabbatar da mayar da yaran makaranta.
Hukumar NAFDAC ta binciki magungunan tare da hana marasa inganci.
Hukumomin tsaro suyi binkince su gano tare da hukunta masu amfani da yara wajen kasuwanci.
abangaren Sarakuna da shugabannin al’umma su wayar da kai domin kawo ƙarshen wannan dabi’a.
Masu sharhin sun bayyana cewa ci gaba da barin wannan lamari ba tare da daukar mataki ba na iya janyo babbar matsala ga al’umma, musamman ganin cewa yaran da ake amfani da su su ne makomar gobe.
Sun jaddada cewa kare yara daga wannan nau’in cin zarafi ba kawai wajibin doka ba ne, har ila yau wajibi ne na tausayi da mutunci.
Daga Ahmad Buhari Aliyu Esq.