Yan Sanda Sun Dakile wani Rikicin fadan Daba a Kano, Sun Kama Mutane 6

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta dakile wani rikici mai hatsari tsakanin wasu gungun ‘yan daba a unguwar Gyadi-Gyadi da ke Kano, inda ta kama mutane shida (6) tare da dawo da zaman lafiya bayan gaggawar daukar matakin tsaro.

 

 

 

 

 

Mai magana da yawun rundunar, yan sada CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2026, inda ya ce lamarin ya faru ne bayan rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 1:20 na rana.

 

 

 

 

A cewar ‘yan sanda, jami’an sintiri sun garzaya wajen da gaggawa, inda suka tarar da tashin hankali tsakanin wasu gungun ‘yan daba masu gaba da juna. An kuma lalata wata motar daukar marasa lafiya (ambulance) yayin rikicin, tare da yunkurin kai hari wasu wurare a kusa kafin jami’an tsaro su shawo kan lamarin.

 

 

 

 

 

Sanarwar ta ce:
“Daga bisani ‘yan daban  sun sake taruwa suka kai wa jami’an tsaro hari da makamai masu hatsari da duwatsu, amma jami’an sun dakile harin cikin kwarewa.”

 

 

 

Rahoton ya kara da cewa bayan sun tsere, wadanda ake zargin sun nufi Kasuwar Farm Centre, inda suka yi yunkurin sace-sace a shaguna.

 

 

 

Daga bisani, rundunar ta tura karin jami’ai, wanda hakan ya kai ga kama mutane shida, yayin da wasu daga cikin ‘yan daba suka tsere.

 

 

 

 

Rundunar ta ce an riga an dawo da doka da oda a yankin.

 

 

 

Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Yi Gargadi
Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin cikin hakuri da kwarewa, tare da gargadin cewa rundunar “ba za ta lamunci duk wani nau’in daba ko tayar da hankalin jama’a ba.”

 

 

 

 

 

Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin kamo wadanda suka tsere da kuma gano masu daukar nauyinsu, yayin da ta bukaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanai a kan lokaci.

You might also like
Leave a comment