Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya nuna farin ciki kan nasarar saukar jirgin gwaji na farko a Filin Jirgin Sama na Gusau.
Mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a wata sanarwa cewa jirgin ya sauka da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a ranar Lahadi.
Ya ce jirgin, kirar Bombardier Challenger 605 wanda gwamnatin tarayya ke sarrafawa, ya gudanar da gwajin sauka ne domin tantance shirye-shiryen filin jirgin, musamman don jigilar manyan baki (VIP) da ake sa ran za su fara amfani da shi nan ba da jimawa ba.
Sanarwar ta ce:
“Wannan rana za ta kasance abin tarihi a Jihar Zamfara, yayin da Gwamna Lawal ya shaida saukar jirgin farko a Filin Jirgin Sama na Gusau.”
An kuma bayyana cewa an gudanar da wannan gwaji ne bisa ka’idojin Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA), musamman sashen dokokin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa.
Kafin gudanar da gwajin, gwamnatin jihar ta nemi izini kuma ta samu sahalewar “No Technical Objection” daga NCAA domin saukar jirgin.
Haka kuma, an gudanar da wannan aiki ne karkashin dokar tashi da saukar jiragen sama ta gani (Visual Flight Rules – VFR), wato a lokacin rana daga fitowar rana zuwa faduwarta.
An bayyana cewa wannan nasara wata babbar alama ce ta ci gaba ga jihar Zamfara, wacce ta kwashe sama da shekaru 30 ba tare da filin jirgin sama ba tun bayan kafuwarta.