Kungiyar tsofaffin Daliban makarantar sakandire ta Goverment senior secondary school warure wadda a yanzu ake kira da Datti Ahmad senior secondary school Aji na shekara 2004 ta gudanarda taron sada zumunci da kuma karrama wasu daga cikin malaman da suka basu gudunmawa a lokaci da suke dalibai a makarantar.

Taron wanda ya gudana a farfajiyar makarantar dake a unguwar Gwale a cikin Birnin kano.

 

 

 

 

Da yake jawabi sakataren tsare tsare na kungiyar saifullah ibrahim yace sun gudanarda taron ne domin kara kulla zumunci da kuma taimaka wa juna musamman a fannoni daban daban na rayuwa, wadanda suka hadarda tallafawa iyalan wadanda suka rasu daga cikin yan wannan kungiyar da aka rayu tare dasu , da kuma tallafawa makarantar .

 

 

 

 

 

 

Daga Cikin tsofaffin malaman da aka karrama sun hadarda malam Nuhu ibrahim, da malam yahaya Ali, malam Ahmad lawan, malam Nasiru. Tukur sai kuma malam Hassan Abubakar.

 

 

 

 

 

Taron ya samu halartar mihimman mutane da suka hadarda wakilin shugaban shiyyar ilimi na yankin karamar hukumar Gwale wanda ya bayyana cewa ma’aikatar ilimi a shirye take ta baiwa wannan kungiyar cikakken goyan baya, domin tallafawa makarantar wajan ganin an inganta harkokin ilimi a bangarori daban daban.

 

 

 

 

 

A karshe an bukaci tsofaffin Daliban da su kara maida hankali wajan samarda ayyukan cigaba a makarantar da suka hadarda bibiyar yadda ake gudanarda ayyuka a makarantar da suka shafi koyo da kayarwa domin samarda ingantaccen ilimi ga Daliban dake makarantar da kuma tallafawa wadanda suke da rauni a cikinsu.

 

 

 

 

 

Daya daga cikin malaman da aka karrama malam Hassan Abubakar ya bayyana farin cikinsa mutuka dangane da yadda wadannan dalibai nasu suka tuna dasu ,suka zabo so aka kuma karrama su da wannan lambar yabo inda yace hakika ilimi shine jigon cigaban kowacce al’umma Inda yayi fatan Alkhairi ga wadanda suka tsara wannan taron.

 

 

 

 

 

A yanzu dai wannan kungiya ta haifarda da manyan mutane a matakai daban daban na rayuwa da suka hadarda malaman jami oi ,manyan maaikata da yan kasuwa .
Shima daya daya cikin Daliban wannan makarantar kamal yakubu Ali ya bayyan ce wa yana mutukar alfaharin kasancewarsa daya daga cikin wadanda suka yi karatu a wannan makaranta wadda ta basu gudunmawa har suka kai matakin da suke a yanzu.

    • daga kamal yakubu Ali.
You might also like
Leave a comment