Iran tace Zata mayar da martani daidai da irin barazanar da aka yi mata

Iran ta ce za ta mayar da martani ga duk wata barazana daidai da irin tasirin da take da shi domin kare kanta, kamar yadda rundunar juyin juya halin Iran IRGC ta bayyana a cikin wata sanarwa.

 

 

 

 

 

 

Wannan na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi na kai hari kan tashoshin wutar lantarkin Iran, tana mai cewa hakan zai kawo tsaiko ga ayyukan jin ƙai kamar asibitoci da cibiyoyin agaji da hanyoyin samar da ruwa da kuma cibiyoyin tace ruwa.

 

 

 

 

 

Sanarwar ta ƙara da cewa idan aka kai hari kan tashoshin wutar lantarkin Iran, to Iran za ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan tashoshin wutar lantarkin ƙasashen yankin da ke samar da wuta ga sansanonin Amurka

 

 

 

 

 

Haka kuma za su kai hari kan cibiyoyin tattalin arziki da masana’antu da makamashi da Amurkawa ke da hannu a ciki.

 

 

 

 

 

 

A cewar IRGC: “Kun kai hari kan asibitocinmu, ba mu mayar da martani ba. Kun kai hari kan cibiyoyin agaji, ba mu mayar ba. Kun kai hari kan makarantunmu, ba mu mayar ba. Amma idan kun kai hari kan wutar lantarki, mu ma za mu kai hari kan wutar lantarki.”

 

 

 

 

 

Rundunar ta kuma musanta zargin da Donald Trump ya yi na cewa Iran na shirin kai hari kan cibiyoyin tace ruwan gishiri.

 

 

 

 

Sanarwar ta ce sojojin Amurka sun kai hare-hare kan cibiyoyin samar da ruwa guda biyar, ciki har da cibiyar tace ruwa ta tsibirin Qeshm, amma IRGC ba ta taba kai irin wannan hari ba.

 

 

 

 

 

Saboda haka ne Iran ta ce za ta mayar da martani ga duk wata barazana daidai da irin tasirin da take da shi.

You might also like
Leave a comment