Tsohon Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya kai ziyara Kano inda ya gana da tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso.

Taron ya gudana ne a gidan Kwankwaso da ke Miller Road, tare da halartar gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da Sanata Seriake Dickson, da kuma mai fafutukar siyasa Naajatu Mohammed, tare da wasu manyan baki.

 

 

 

 

 

Ziyarar ta jawo hasashe kan yiwuwar sabon sauyin siyasa, inda ake rade-radin cewa Kwankwaso na iya barin jam’iyyar NNPP ya koma ADC.

 

 

 

 

 

Da yake jawabi yayin bikin Sallar Kwankwasiyya, Obi ya ce zuwansa Kano domin taya murna ne da kuma girmama Kwankwaso, tare da jaddada kudurinsa na farfaɗo da tattalin arzikin Kano.

 

 

 

 

 

 

Ya ce:
“Mun zo ne domin taya ku murnar Sallah da kuma girmama jagoranmu.”

 

 

 

 

 

Ya ƙara da cewa:
“Muna son mu sauya Kano, mu gina sabuwar Kano. Abin da muke so shi ne mu dawo da ƙarfin Kano — dukkanin masana’antun da ke Bompai, Sharada 1, Sharada 2, da Bank of the North — muna son mu dawo da su. Yau ba siyasa ba ce, bikin Sallah ne kawai.”

 

 

 

 

 

A nasa bangaren, Kwankwaso ya tarbi baƙin tare da nuna farin ciki kan wannan haɗin kai da aka nuna a lokacin bikin Sallah.

You might also like
Leave a comment