Gwamnan Kano abba kabir yusuf Ya Sauke Shehu Wada Sagagi daga Mukaminsa na Kwamishinan
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga nadinsa a matsayin Kwamishinan Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu nan take.
Sanawar na dauke da sahannun magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Alhamis 26-3-2026
A cewar sanarwar, an umarci tsohon Kwamishinan da ya mika harkokin ma’aikatar ga Daraktan Kasuwanci nan take.
Gwamna Yusuf ya nuna godiyarsa ga ayyukan da tsohon Kwamishinan ya yi a lokacin da yake kan mulki.
Ya yabawa kwamanshinan bisa irin gudummawar da yabayar alokacin aikin sa , musamman a fannonin siyasa, addini, kananan da matsakaitan kasuwanci.
Gwamna ya yi masa fatan samun nasara a ayyukansa na gaba yayin da yake tabbatar wa jama’a cewa gwamnatinsa na ci gaba da jajircewa wajen samar da ayyuka masu inganci da kuma shugabanci nagari a jihar.
Wannan. nazuwane a matsayin wani bangare na ci gaba da daidaita tsarin gwamnati don ci gaba mai dorewa.