Rundunar ‘Yan Sanda jahar bauchi Ta Tura Manyan Jami’an Tsaro Zuwa Alkaleri
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta bayyana cewa ta tura dimbin jami’an tsaro tare da ingantattun makamai zuwa al’ummomin da ke fama da matsalar tsaro a Karamar Hukumar Alkaleri domin dakile ayyukan ‘yan bindiga da kuma hana tabatar da…
Shugaba Tinubu ya buƙaci majalisa ta gyara ƙundin mulki domin kafa ‘yansandan jihohi a Nigeria
Shugaban kasa , Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugabannin Majalisar Dattawa su fara nazarin yiwuwar gyaran ƙundin tsarin mulki domin samar da dokar da za ta ba da damar kafa ‘yansandan jihohi, a wani yunkuri na magance matsalolin rashin…
Da dumi dumi DSS Ta Saki Walida
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karɓi Walida Abdulhadi Ibrahim wacce ta ɓace tun shekarar 2023 kuma take a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).
Gwamnan ya tabbatar da cewa za a tabbatar da adalci kan…
Gwamnatin jahar kano zatafara shirin yaki da cutar zanzabin. tsintsaye (Avian Influenza)
Ma’aikatar Raya Kiwo ta Jihar Kano, karkashin jagorancin Kwamishina, Dr. Aliyu Isah Aliyu, na shirin fara aiwatar da Kashi na Farko na Shirin Yaki da Cutar Zazzabin Tsuntsaye (Avian Influenza – AI), bayan amincewar Mai Girma Gwamnan…
Wani SSR din gwamnatin jahar kano yaci zarafin wani dan jarida agaban manyan jamian gwamnati
Wani dan jarida daga Jihar Kano ya bayyana shirin kai kara kotu biyo bayan zargin cin mutuncinsa da wani jami’in gwamnatin jihar ya yi a yayin gudanar da bakin tsaren motoci a wani bangare na gasar Kamun kifi da ake gudanarwa a garin…
Shugaba Tinubu Ya Sallami Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami Kayode Egbetokun daga mukaminsa na Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya (IGP).
Wasu majiyoyi daga cikin Police Service Commission sun tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar…
Shugaban kasa bola tinibu yace Dole ne a gyara abubuwan da ba sa aiki a Najeriya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce dole ne a gyara abubuwan da ba sa aiki a ƙasar tare da haɗin gwiwar ƴan kasa domin tabbatar da ci gaban al’umma da tsaron rayuka.
Tinubu ya fadi hakan ne a walimar buɗe…
Rundunar ‘yansanda ta kama wadanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a garkuwa da mutane tare da samar wa ‘yan bindiga kayan abinci da sauran kayan tallafi.
Wadanda aka kama sun hada da Abubakar Sindiku mai shekaru 25 da…
Jam iyyar adawa ta PDP za ta kai APC kotu kan zaɓen Abuja
Jam’iyyar PDP ta sanar da kafa wata ƙungiyar lauyoyi ta musamman domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a yankunan babban birnin tarayya, Abuja.
Matakin na zuwa ne bayan sakamakon…
Kungiyar tarayyar africa AU ta yi allawadai da kisan fiye da mutum 50 a Zamfara
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta yi allawadai da abin da ta kira munanan hare-haren ƴan bindiga da aka kai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda aka kashe fiye da fararen hula 50 tare da sace mata da yara da dama.
…
zargin laifukan zaɓe a Abuja EFCC ta kama mutum 20
Hukumar EFCC ta sanar da kama mutum 20 da ake zargi da aikata laifukan zaɓe yayin zaɓen ƙananan hukumomin babban birnin tarayya, Abuja da aka gudanar a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.
EFCC. Ta ce ta kama su ne…
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubukar ya nuna damuwarsa kan karancin fitowar jama,a. A…
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan ƙarancin fitowar jama’a a zaɓen Ƙananan Hukumomin Babban Birnin Tarayya da aka gudanar ranar Asabar, yana mai cewa hakan alama ce da ke nuna dimokuraɗiyya na shaƙewa a…
Babbar Alkaliyar Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun, za ta rantsar da sabon Alkalin Kotun Koli, Joseph…
Bikin rantsuwar Zai gudanar ne a Kotun mai Lamba Biyu da ke harabar Supreme Court of Nigeria a Abuja da misalin ƙarfe 2 na rana, inda ake sa ran manyan alkalai za su halarta.
Jaridar Daily Trust ta…
Ƙasashen Larabawa sunyi allah wadai kan kalaman jakadan Amurka a Isra’ila
Gwamnatocin ƙasashen Larabawa da na Musulmi sun yi alla-wadai da kalaman jakadan Amurka a Isra'ila Mike Huckabee, wanda ke nuni da cewa Isra'ila za iya mamaye yanki mai faɗin gaske a gabas ta tsakiya bisa hujjar Littafin Injila.
…
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wadanda ake zargi da satar motoci
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta samu gagarumar nasara a yaki da satar ababen hawa, bayan kama wata ƙungiyar mutane shida da ake zargi da satar motoci tare da ƙwato motoci uku da aka sace.
A cewar sanarwar…